Shugaba Bola Tinubu na shirin bayyana sabon mafi karancin albashin ma’aikatan Najeriya nan da mako mai zuwa, kamar yadda Comrade Festus Osifo, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) ya bayyana.
Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (TUC), Kwamared Festus Osifo ne ya bayyana hakan a lokacin da yake magana kan sakamakon taron kungiyar da gwamnatin tarayya kan cire tallafin man fetur.

Idan zaku iya tuna, kungiyar TUC ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin makonni biyu don magance bukatunta ko kuma ta sake Tsunduma yajin aikin a fadin kasar.
Da yake magana a gidan talabijin na Channel cikin shirin Politics Today, Osifo ya bayyana cewa ministan kwadago, Simon Lalong, ya shaida musu cewa ya gana da shugaba Tinubu da ministan kudi, Wale Edun.
Osifo ya ce Lalong ya shaida wa kungiyar cewa an sake duba batun albashin inda ya ce shugaba Tinubu zai yi magana kan lamarin nan da kwanaki masu zuwa.
. Amma shugaban ya bukaci su gyara al’amuran kafin ya bayyana,” in ji shugaban TUC.
“Ministan ya ce mana duk wadannan batutuwa za a daidaita su, amma saboda shugaban kasa ya yi tafiya ya kamata mu ba shi karin mako biyu.
Muka ce a’a; ba mu da ƙarin makonni biyu don bayarwa.
Bayan karin tattaunawa, ya ce shugaban zai yi sanarwar da ta dace a mako mai zuwa.”
Osifo ya lura cewa kungiyar ta lura da gwamnatin tarayya kan ayyukan jin kai da aka rabawa jihohi.
“Za mu sanya ido kan yadda ake rarraba kayayyakin jin dadin jama’a a jihohi domin tabbatar da an aiwatar da shirin yadda ya kamata.
Muna son ganin samfurin aiwatarwa wanda shine dalilin da ya sa muka tsunduma gwamnatin tarayya kan wannan batu.
Mun kuma tabo batutuwan da suka shafi haraji da CNG (Compressed Natural Gas),” in ji shugaban TUC.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb
ALLAH YASA HAKAN YA ZAMEWA JAHAR KANO ALKHAIRI,ALLAH YAYI RUKO DA HANAYAN SA,YA BASHI IKON SAUKE NAUYIN DA ALLAH YA DORA MASA, ALLAHUMMA AMEEEEEN
Amin ya Allah ya rabbal alamin
Idan anyikarin salary mamaaikata sauranyankasafa talakawafa mealashiryamusu gwandama masu albashi dukdadai salary is not enough xasuiya manage dukdadaibahaka akasoba worse part sunetalakawa marassa aikinyI sumakuma kiwoneda Allah yabawa shigabansu yanxuxabe yawuce ammantadasu Allah yamaname bayabarci