Alkalai da Shugabanni kuji tsoron Allah kan hukuncin kano – in Ji Young Sheikh Zariya

Don Allah Gwamnati da Jami’an Tsaro tare da Alkalai Kuji Tsoron Allah ku yiwa Kano da kanawa Adalci.

Alfijir Labarai ta rawaito young Sheikh Zariya na cewar, idan za a raba gadon Kano akwai nawa kaso dan haka ina da ta cewa kan hukuncin kotu Young Sheikh

Kano Garin Ilimi, Kano Garin Kasuwanci, Kano Garin Soyayyar Manzo (S.A.W) a cewar matashin Shehin Young Sheikh Zariya.

Ya ƙara da cewa haƙiƙa duk wanda kaga yana tanajin tàshin Hankali Lallai ba Bakano Bane Bakon Haure Ne!

Kuma ba zamu lamunci mutane su ɓoye a garin Abuja, Su din ga kunno mana wuta a Kano su kuwa da iyalansu sun tare a Abuja.

Musani mufa kanawa ƴan uwan juna ne, Kasuwa, Makarantu Da asibitocin mu duk a Kanon ne.

Su kuwa wadanda muke Kishi Ko goyon baya a siyasar, hidimominsu na Abuja ko Ingila, Kar mu yarda a ɓata mana Kano Domin Ita Kadai Garemu a Arewa.

Don Allah Gwamnati da Jami’an Tsaro tare da Alkalai Kuji Tsoron Allah ku yiwa Kano da kanawa Adalci.

Tabbas nima bakanone ta wurin mahaifiya ta, don haka koda rabon gadon Kano a kayi za’a bani ta mahaifiya ta.

Munawa kanawa fatan nasara da zaman lafiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *