Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauya wa wasu filayen jiragen saman tarayya sunayen wasu fitattun ‘yan Najeriya.
Alfijir Labarai ta rawaito an bayyana sauya sunayen filayen jiragen saman ne a cikin wata takarda da ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya ta fitar mai dauke da kwanan watan 1 ga watan Yuni 2023, mai dauke da sa hannun Misis Joke Olatunji a matsayin daraktan ayyuka na filin jirgin a ranar Litinin 26 ga watan Yuni, 2023.
Sanarwar ta nuna cewa shugaban kasar ya canza sunan filayen jiragen sama “a matsayin wani bangare na sake fasalin bangaren sufurin jiragen sama.”
An sauya sunan filin jirgin saman Maiduguri da sunan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da filin jirgin sama na Fatakwal da sunan marigayi dan kishin kasa Obafemi Awolowo, yayin da filin jirgin na Nasarawa marigayi Usman Dan Fodio wanda ya kafa Daular Sokoto.
Har ila yau, an sauya sunan filin jirgin sama na Benin da sunan marigayi Oba na Benin, Oba Akenzua II, da filin jirgin Ebonyi da sunan marigayi shugaban majalisar dattawa, Chuba Okadigbo, da kuma filin jirgin saman Ibadan da sunan marigayi Firimiya na tsohuwar yankin Yamma, Ladoke Akintola.
Gasu kamar haka :
- Akure Airport – Olumuyiwa Bernard Aliu
- Benin Airport – Oba Akenzua II
- Dutse Airport – Muhammad Nuhu Sanusi
- Ebonyi Airport – Chuba Wilberforce Okadigbo
- Gombe Airport – Brigadier Zakari Maimalari
- Ibadan Airport – Samuel Ladoke Akintola
- Ilorin Airport – Gen. Tunde Idiagbon
- Kaduna Airport – Hassan Usman Katsina
- Maiduguri Airport – Gen. Mumammadu Buhari
- Makurdi Airport – Joseph Sarwuan Tarka
- Minna Airpor – Mallam Abubakar Imam
- Nassarawa Airport – Sheikh Usman Dan Fodio
- Osubi Airport – Alfred Diete Spiff
- Port Harcourt Airport – Obafemi Jeremiah Awolowo
- Yola Airport – Lamido Aliyu Mustapha.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ