Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Laraba 28 ga watan Yuni da Alhamis 29 ga watan Yuni 2023 a matsayin ranakun hutun jama’a.
Alfijir Labarai ta rawaito babban Sakatare a maโaikatar harkokin cikin gida, Dakta Oluwatoyin Akinlade, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Litinin a Abuja, ya ce an bayyana hakan ne domin tunawa da bikin Eid-el-Kabir na bana.
โA cikin wannan biki na musamman, wanda muke tunawa da manya-manyan kyawawan halaye na biyayya, sadaukarwa da imani kamar yadda Annabi Ibrahim (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), da Musulmi, da kuma dukkan โyan Nijeriya an umurce su da su yi sadaukarwa domin ci gaban al’ummarmu da babbar kasarmu Najeriya.
“Muna fatan addu’o’i da sadaukarwa da suka zo tare da wannan gagarumin biki da kuma sakon Eid-ei-Kabir za su kawo zaman lafiya, hadin kai da ci gaba a Najeriya,” in ji sanarwar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai ๐
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ