Shugaba Tinubu Ya Sake Magantuwa Akan Cire Tallafin Man Fetur A Najeriya

Halin da muke ciki a kasar mu yau, shine domin kyakkyawan gobenmu

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hakuri da gwamnatinsa dangane da cire tallafin man fetur, yana mai cewa matakin na da amfani ga kasar.

Tinubu ya yi magana ne a Abuja ranar Alhamis yayin da yake gabatar da tarihin rayuwar wani dattijon jihar, Edwin Clark.

Shugaban na Najeriya wanda sakataren gwamnatin tarayya George Akume ya wakilta a wajen taron, ya ce ana kokarin shawo kan illar cire tallafin.

Na san cire tallafin man fetur ya haifar da wasu abubuwa.

Kuma shi ya sa aka sanya kayayyakin jin kai a madadin manyan motoci 100 da aka niyyar siya. In ji Tinubu

. “An aika da taki zuwa Jihohi, an aika da tireloli na hatsi 100 wasu karin ma na nan zuwa.

Don haka za mu iya jure wa wannan na ɗan lokaci.

Abinda muke ciki a yau shine don ingantacciyar gobenmu.

Al’ummai suna da girma saboda ‘yan ƙasa suna fatan gobe za ta fi yau.

Kalaman nasa na zuwa ne biyo bayan amincewar da gwamnatin tarayya ta yi na samar wa gwamnatocin jihohi yanayin da zasu taimaki al’ummar su.

Bayan taron da ta yi a fadar shugaban kasa, Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) ta amince da Naira biliyan 5 ga kowace jiha da birnin tarayya Abuja da kuma hatsi ga gwamnonin jihohi.

Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya ce gwamnati ta kuma saki motocin shinkafa guda biyar kowacce ga gwamnonin jihohi 36.

Ya kuma ce ana sa ran gwamnonin za su sayi buhunan shinkafa 100,000, buhunan masara 40,000, da takin zamani a wani mataki na dakile illar cire tallafin man fetur.

Zulum ya kara da cewa kashi 52 cikin 100 na kudaden an rabawa jihohi ne a matsayin tallafi.

Sauran – 48 bisa dari – ana ganin su a matsayin lamuni.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *