Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya dauki matakai don dakatar da yunkurin Shoprite daya daga cikin fitattun manyan kantunan Najeriya daga rufe reshensa na jihar Kano.
Alfijir labarai ta rawaito Shahararren kantin sayar da kayayyaki na Shoprite dake Ado Bayero Mall ya sanar da matakin rufewa daga jihar Kano a watan Janairu, inda ya dora laifin ga yanayi na kalubalen tattalin arziki.
Jama a da dama suna ta bayyana ra’ayoyinsu dangane da hukuncin da kantin ya dauka, wanda kuma ya fara gudanar da harkokin kasuwancin sa a Kano a watan Maris na 2014.
Wata sanarwa da mai baiwa Sanata Barau shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Ismail Mudashir ya fitar, ta ce mataimakin shugaban majalisar dattawan zai gana da mahukuntan kamfanin a cikin makon nan a Abuja don shawo kan lamarin.
‘’ Eh, batun kasuwanci ne tsantsa, amma za mu ga abin da za mu iya yi don karfafa musu gwiwa su janye shawarar da suka yanke ta barin Kano, don su ci gaba da zama a birnin na dabo.
Tabbas kamar yadda kowa ya sani, akwai tarin damammakin kasuwanci a cibiyar kasuwanci ta Arewacin Najeriya. In Ji sanatan, don haka zamu yi mai yiwuwa wajen daidaita lamarin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp