Takaitattun Labaran Yammacin Duniya Na Litinin 18/12/2023 – 04/06/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Kotun Ƙoli ta sanya ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba domin sauraron ƙarar da aka shigar kan zaɓen gwamnan jihar Kano.

Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da nasarar Fintiri a matsayin Gwamnan jihar Adamawa.

Hukumar JAMB ta kara kudin jarabawar daga N5,700 zuwa N7,700 a wata sanarwa da ta raba wa manema labarai.

Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani ya bai wa al’ummar musulmi da kirista da ke jihar tabbacin cewa gwamnatinsu za ta yi wa kowa adalci.

An kama dabbobi 90 daga hannun dan fashi a Kaduna.

Akalla mutum biyu suka mutu a wata gobara da ta tashi a gidan tsohon gwamnan jihar Oyo, marigayi Adebayo Alao-Akala.

Tsohon Gwamnan Filato Simon Lalong ya ajiye mukaminsa na minista a hukumance domin ya karbi kujerar sa ta majalisar dattawa.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani malami a kwalejin ilimi ta jihar Zamfara da ke Maru bayan karbar kudin fansa har naira miliyan biyu.

Wata kotun Musulunci a Kano ta tsare wasu mutum hudu da ake zargi da yin ludo da shaye shaye a cikin masallaci.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu garkuwa da mutane sun sace wani mawaki da masu masa kida a hanyar Abuja zuwa Kogi.

Abdel Fattah al-Sisi ya lashe zaɓen shugaban Masar karo na uku.

An shiga rana ta ƙarshe ta yaƙin neman zaɓe a Congo.

Sojojin Somalia sun karɓi aikin samar da tsaro a Fadar shugaban ƙasar da ginin majalisar dokoki da ke Mogadishu daga hannun tawagar wanzar da zaman lafiya ta tarayyar Afirka bayan shekara 16.

Akalla mutane 8 suka mutu, yayin da wasu 84 kuma suka jikkata sakamakon fashewar wani abu a tashar mai da ke Conakry a kasar Guinea.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *