Ana cikin dar-dar a Kano yayin da ake dakon hukuncin Kotun Koli a yau Juma’a 12 ga watan Janairu
Alfijir labarai ta rawaito Rundunar ‘yan sanda a jihar ta ba da tabbacin samar da tsaro a wurare da dama don dakile tashin hankali. Wannan na zuwa ne yayin da Kotun Koli ta sanya yau Juma’a a matsayin ranar yanke hukuncin karshe na Jihar.
Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Hussaini Gumel shi a bayyana haka a yayin ganawa da ‘yan jaridu a Kano ranar alhamis. Gumel ya ba da tabbacin cewa za su ba da tsaro kafin lokacin da kuma bayan sanar da sakamakon shari’ar gwamnan jihar.
Kwamishinan ya ce rundunar ta samar da wani yanayi don bai wa mutane damar gudanar da harkokinsu ba tare da matsala ba, “Mun samar da jami’an tsaro a ko ina don samar da tsaro a wasu wurare na musamman.
“Wuraren sun hada da ofisoshin jam’iyyun siyasa da gidan gwamnati da hukumar INEC da bankuna da kasuwanni.
“Sauran sun hada da wuraren ibada da wuraren shakatawa da tashoshin mota da sauransu.” Ya ce ya ba da tabbaci wa jama’a samun tsaro dari bida dari inda ya bukaci mutane su fita harkokinsu ba tare da wata matsala ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl