Yadda Ma aikacin Bankin UBA Ya Sace Min Miliyoyin Kudade A Asusuna A Kano – In Ji Garzali Yakasai

IMG 20240111 WA0148

Wani matashin dan kasuwa mai suna Garzali wada Ibrahim Yakasai cikin birnin Kano, ya bayyanawa Jaridar Alfijir labarai yadda lamarin ya faru.

Ina ajiya da wannan Bankin sama da Shekaru goma Sha biyu, na sai matsala da Mobile app dina sai naje Bankin UBA na sharada kano domin su gyara min, sai wani ma aikacinsu Mai suna OSAKA OMADA ya karbi wayata yace na zauna zai duba min.

Bayan dan lokaci sai ya miko min wayar yace na saka code dina, sai nace ya aka yi ka fitomin da account number ta, har ka Iya ganin abinda ke ciki? Sai yace ai idan suka yi wannan gyaran suna ya gani bawata matsala.

Sai yace na saka code dina, yana tsaye a kaina na saka yana kallo kuma yayi daidai, nan na gwada tura 20k kuma suka tafi babu wata matsala.

Da garin Allah ya waye sai kawai naga an daukarmin dubu dari uku da casa in (N390 000) sai na nunawa wanda muke tare da shi, ana haka sai kuma naga an sake cire miliyan miliyan har sau uku gaba daya miliyan uku da dubu dari uku da casa in! (N 3,390,000)

Ranar da lamarin ya faru babu aiki ana komawa aiki sai na Isa wajen manaja na shaida masa abinda ma aikacinsu yayi min, nan dai manaja yace ba haka bane, domin ma aikacinsu ba zai yi wannan aikin ba, bayan dogon zance suka karbi account number Dina suka ce bayan kwana biyu na dawo domin suna cikin wani aiki a lokacin.

Da ranar tayi nan ma na koma suka dinga yawo da hankalina babu wata magana mai dadi.

Daga karshe dai na je na shaidawa yan sanda aka zo aka tafi dashi, daga karshe dai ma aikatan Bankin suka karbe shi beli da zummar washegari za su kawo shi da bayanin asusuna.

Da suka kawo sai gashi nan inda aka cire kudaden ga inda aka kai su, sai na tambayesu to wanene ya tura? Nan aka ce na bari sai sati Mai zuwa.

Nan dai satin ya cika shiru nan ma aka kara cewar sati biyu wai basu gama bincike ba.

Kashi na farko na kudaden da aka sata sun kai kimanin 2,000,000 inda aka tura su zuwa asusun bankin Wema mai lamba 7790847364 mai dauke da sunan BSTPOS-Musa.

Haka zalika kashi Na biyu na kudin da aka cire ya kai kimanin 1.300.000 inda aka tura shi zuwa asusun Opay mai lamba 9068129712 mai suna Angela Anulika weke

Shine nake roko da mahukunta da su dubi Allah su dubi Annabi a taimakeni a nemar min hakkina, wasu daga cikin masu kudaden nan nima sun fara daga min hankali Wasu ma sun kaini ga Hukuma.

IMG 20240111 WA0199
Complain Letter

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai πŸ‘‡πŸ‘‡

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *