Mataimakin sufeton yan sandan Nijeriya shiya ta daya dake jahar Kano, AIG Umar Mamman Sanda, ya bayyana cewa zaben da za a gudanar a ranar Asabar 3/2/2024, ya shafi Kananan hukumomin, Kunchi, Tsanyawa, Kura, Garin malam, Tofa, Rimin gado, Birnin Kudu da Kuma Buji dake jahohin kano da Jigawa, inda suka shirya tsaf don tabbatar da tsaro.
Alfijir labarai ta rawaito Mai magana da yawun rundunar shiya ta daya CSP Bashir Muhammad , ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a yau Juma’a,
CSP Bashir Muhammad, ya ce an takaita zirga-zirgar ababen hawa, a dukkanin wuraren da zabukan ya shafa.
Sanarwar ta shawarci yan siyasa da magoya bayansu da su kiyaye da ka’idojin hukumar zabe, domin ba za a bar kowa ya yi abunda ya saba da doka ba.
Haka zalika rundunar shiya ta dayan, ta kara da cewa, za su yi aiki da sauraran hukumomin tsaro, don ganin an tabbatar da tsaro kafin zaben da ma bayansa, kamar yadda babban sufeton yan sandan Nijeriya ya bada umarni.
A karshe rundunar ta yi fatan za a bada hadin kai domin gudanar da aiyukan zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V