Takaitattun Labaran Duniya Na Yammacin Juma’a 21/07/1445AH – 02/02/2024CE

IMG 20240103 WA0021

Daga Baba Usman Gama

Kotu a Abuja ta amince da tuhumar ta’addanci ga magoya bayan Gwamman jihar Ribas Fubara.

CBN na zargin bankuna da sayar da Dala ta bayan fage.

Jami’ar kimiya da Fasaha dake Wudil a jihar Kano ta kirkiri mutum mutumi.

Masu gurasa sun yi zanga-zanga kan tsadar fulawa a Kano.

An yanke wa wata ƴar fim ɗin kudacin Najeriya hukuncin ɗaurin watanni 6 a gidan yari, bayan da aka ɗauki hotonta tana liƙa sabbin takardun kuɗin naira da aka fitar a bara, tare kuma da taka su.

Masu satar mutane a Abuja sun buƙaci babura 2 bayan karɓar naira miliyan 8.6.

Gwamnatin Jigawa za ta rinka bai wa ma’aikata karin dubu 10 duk wata.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wasu mutum 12 da ake zargi da buga jabun kudi a jihar.

Majalisar jihar Oyo ta bukaci cafke shugaban Fulani kan zargin kisan manomi da jami’in tsaro.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta cafke wasu mutum biyu da ake zargi da satar man dizal din taransufoma a Karamar Hukumar Jakusko a jihar.

Jiragen saman Nijar sun daina dibar fasinjojin Faransa.

Kasar Ghana ta fara karbar haraji kan ababan hawa masu hayaki.

Mali ta dakatar da tashar talabijin ta Faransa kan zargin ingiza ta’addanci.

Kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar, sun fice daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS).

Gwamnatin Indiya ta rushe babban Masallacin Akhonji da aka gina shekaru 600 da suka gabata a birnin New Delhi, domin a gina wurin bautar mabiya addinin Hindu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *