Rundunar ‘yan sandan Najeriya, babban birnin tarayya Abuja, ta kama wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a kisan Sadiq dan Kabiru Gaya, sanata mai wakiltar Kano ta Kudu.
Alfijr Labarai
Sadiq dai ya rasu ne a ranar Talata kuma ba a san halin da ya kai ga mutuwarsa ba.
Da take tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya, Josephine Adeh, ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kuma mutane biyar da ake zargi suna hannun ‘yan sanda.
“An kama mutane biyar da ake zargi da aikata laifin, kuma ana ci gaba da bincike,” in ji ta.
Ta kara da cewa “Za a sanar da sakamakon binciken daga baya.”
Tun da farko mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jajanta wa Sanatan kan lamarin.
Alfijr Labarai
Gaya shi ne darakta-janar na kungiyoyin goyon bayan Osinbajo a lokacin da mataimakin shugaban kasar ke neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
“Wannan ziyara ce mai matukar ban tausayi. Sadiq saurayi ne. Ya kasance kamar ɗa a gare ni,” in ji Osinbajo.
Ina mika ta’aziyya da kuma jajanta wa mai girma Sanata da daukacin iyalansa da gwamnati da al’ummar Jihar Kano da suka yi rashin dansu mai kima a wannan matashi.
Masha Allah inajin dadin kasancewa daku dayanda kuke gabatar d shiryeshiryenku
Masha Allah Allah ya faranta