Hukumar Tsaftar Muhalli da Kwashe Shara ta Jihar Kano (REMASAB), ƙarƙashin jagorancin Manajan Darakta, Dakta Muhammad S. Khalil, ta kaddamar da Asibitin AKY domin kula da lafiyar ma’aikatan hukumar. Wannan muhimmin shiri wani ɓangare ne na ƙoƙarin hukumar na inganta jin daɗi da walwalar ma’aikatanta tare da samar musu da kulawar lafiya mai inganci.
Da yake jawabi a wajen taron ƙaddamarwar, Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya yaba wa Manajan Daraktan REMASAB bisa jajircewarsa wajen kula da walwalar ma’aikata da kuma gudanar da harkokin hukumar cikin kwarewa.
Ya ce, “Ya zama wajibi in yaba wa abokin aikina bisa yadda yake nuna ƙwarewa da jajircewa wajen tafiyar da wannan hukuma, tare da ba da fifiko ga jin daɗin ma’aikatanta.”
Haka kuma, ya yi kira ga ma’aikatan hukumar da su ci gaba da bai wa shugabancinsu cikakken goyon baya domin tabbatar da dorewar tsafta da kyakkyawan muhalli a faɗin Jihar Kano.
Shi ma da yake nasa jawabin, Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Dabbobi ta Jihar Kano, Dakta Aliyu Isah Aliyu, ya jaddada aniyar ma’aikatarsa na ci gaba da haɗin gwiwa da REMASAB wajen tabbatar da tsafta a kasuwannin dabbobi, mayanka da sauran wuraren da suka shafi harkokin dabbobi.
A nasa jawabin, Manajan Daraktan REMASAB, Dakta Muhammad S. Khalil, ya bayyana yadda asibitin zai gudanar da ayyukansa. Ya bayyana cewa an yi wa dukkan ma’aikatan hukumar rijista a Hukumar Kula da Lafiya ta Taimakon Juna ta Jihar Kano (KSCHMA) ƙarƙashin shirin Abba Care, domin sauƙaƙa musu samun ingantaccen kulawar lafiya.
Dr Khali ya Kara da cewa “An yi wa dukkan ma’aikatan wannan hukuma mai daraja rijista a KSCHMA. Asibiti zai riƙa gudanar da duba lafiyar ma’aikata da kula da ƙananan matsalolin lafiya. Duk wata cuta ko matsalar da ta zarce ƙarfin asibitin, za a tura mara lafiya zuwa manyan asibitocin gwamnati kamar Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da sauran makamantansu.”
A wani ci gaba kuma, hukumar ta samar da wutar lantarki ta hasken rana mai aiki na sa’o’i 24 a hukumar Remasab.
Wannan na daga cikin manufofin Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf na inganta ababen more rayuwa da kuma kyautata ayyukan gwamnati.
Taron ƙaddamarwar ya samu halartar manyan daraktoci, jami’an gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki a bangare lafiya na jiha da abokan hulda na ketare (partners).
Sanya Hannu:
Abubakar Ahmad
Jami’in Hulɗa da Jama’a (P.R.O.)
REMASAB, Kano.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t