Obasanjo ya caccaki alkalai kan hukuncin shari’ar zaɓen gwamnoni

Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya caccaki hukuncin da alƙalan Najeriya suka yanke kan shari’o’in zaɓe, yana mai cewa bai kamata alƙalai uku zuwa biyar su soke hukuncin da miliyoyin masu kada ƙuri’a suka yanke a lokacin zabe ba.

Alfijir Labarai ta rawaito Obasanjo ya bayyana ikon da wasu alƙalai ƙalilan ke da shi a matsayin al’amari da “ba za a amince da shi ba.”

Tsohon shugaban ƙasar ya yi magana ne dangane da hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ke ci gaba da yi kan taƙaddamar zaɓe ta bayan zaɓen 2023 a Najeriya.

A makon da ya gabata ne dai wasu alƙalan kotun ɗaukaka ƙara suka yanke hukuncin korar wasu gwamnoni uku daga aiki.

Lokacin da yake tsokaci a wani taro sake fasalin dimokuraɗiyya domin amfanin ƙasashen Afirka, a garin Abeokuta na jihar Ogun, ya ce tsarin mulkin dimokuraɗiyya na ƙasashen yamma ba zai taɓa yin daidai da ƙasashen Afirka ba kasancewar ba ya la’akari da ra’ayin mafi yawan al’umma.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *