Iftila’i: Gobara ta tayi Mummunar barna a hukumar Shari’a ta jihar kano

IMG 20231121 WA0002

Gabora ta tashi a wani bangare na hukumar shari’a ta jihar kano a yau Talata, lamarin da ya janyo asarar dukiya mai tarin yawa a ofisoshin dake bangaren.

Alfijir Labarai ta rawaito Hajiya Batulu Isah Waziri babbar daractan kudi da mulki ta tabbatar da faruwar lamarin, Inda ta ce wutar ta faraci misalin karfe 01:30 dai dai lokacin da aka shiga sallar azuhur.

Ta ce wutar ta kone ofisoshin da ke ɓangaren, amma ba a samu asarar rai ba, sai dai ta dukiya.

Jami’an kashe gobara sun sami nasar kashe gobarar bayan da jami’an mu suka sanar da su faruwar lamarin. In Ji Batulu

Hukumar shariah dai itace hukumar da ke kula da abin da ya shafi harkokin addini, masallatai
da makarantun addini da abinda ya shafi lokutan sallah da Nisabin zakka da sauransu.

IMG 20231121 WA0004
Kano Shari’ah Commission
IMG 20231121 WA0001
Kano Shari’ah Commission

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *