Alfijr ta rawaito NCAA ta ce kamfanin jiragen sama na Azman ya gaza sabunta takardar shedar Air Operator (AOC) daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA).
Alfijr Labarai
Wannan dalili ne hukumar ta dakatar da lasisin aiki na kamfanin har zuwa wani lokaci a cewar hukumar.
AOC kayan tsaro ne na jirgin sama wanda ke ba da izinin ma’aikacin jirgin sama don aiwatar da takamaiman ayyukan jigilar jiragen sama na kasuwanci.
Hukumar NCAA na sabunta takardar shaidar duk bayan shekara biyu a Najeriya.
Alfijr Labarai
Alfijr ta ji ta bakin daracta operation na kamfanin Alh Nura, wanda ya tabbar Labarai da cewar, ba dakatar dasu aka yiwa ba, sune don radin kansu saka restarts da ayyukansu na yau don sabunta lasisin nasu, amma zuwa gobe cikin ikon Allah za sun Ci gaba daga in da suka tsaya