
Alfijr ta rawaito Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da farashin jigilar maniyyata aikin hajjin 2023 zuwa kasar Saudiyya.
Shugaban Hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan, da yake sanar da sabon farashin kudin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a a Abuja, ya ce kudin na bana bai daya kamar da, inda ya ce farashin ya bambanta da jihohi.
A cewarsa, kowane mahajjaci da ya fito daga Maiduguri da Yola zai biya Naira miliyan biyu da dubu dari takwas da casa’in.
Mista Hassan, ya ce mahajjatan da suka fito daga wasu jihohin Arewa za su biya Naira miliyan 2,919,000.

Ga Jihohin Kudu Maso Gabas da Kudu-maso-Kudu ban da Kuros Riba, maniyyatan da ke niyyar zuwa aikin Hajji za su biya Naira 2,968,000.
Alhazan Kuros Riba masu niyyar zuwa Hajji za su biya Naira 2,943,000,” in ji shugaban.
Yayin da maniyyatan jihohin Ekiti da Ondo za su biya Naira miliyan biyu da dubu dari takwas da tamanin da takwas, yayin da maniyyatan jihohin Legas, Ogun da Oyo za su biya Naira miliyan 2,993,000 kowanne.
Shugaban hukumar ta NAHCON ya kara da cewa ranar 24 ga watan Afrilu ne wa’adin kammala aikin Hajji, inda ya jaddada cewa ba za a samu karin ranakun da za a yi ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ