Mutane 2 sun Mutu Wasu Sun Jikkata Yayin Da Ƴan Ƙungiyar Asiri Suka Yi Ta Harbe-Harbe

Alfijr ta rawaito Mutane biyu sun mutu, da dama sun jikkata yayin da wasu ‘yan kungiyar asiri suka yi ta harbe-harbe da bindiga a Osogbo, babban birnin jihar Osun

An tattaro cewa wani fitaccen dan kungiyar asiri kuma dan kasuwa mai suna ‘Kokoro’ ya bar kungiyar asiri, don haka ‘yan kungiyarsa suka yi awon gaba da shi.

A lokacin da labarin sace shi ya bazu cikin al’ummarsa da ke kewayen Ita-Olokan, sai ‘yan kungiyarsa suka yi tattaki zuwa yankin Oke-Baale inda aka kai shi.

Wani ganau mai suna Usman Adeola da ke zaune a yankin ya ce, babu wata alama da ke nuna cewa rikici ya barke a tsakanin al’umma har sai da karar harbe-harbe da jama’a suka ji, suka yi ta tururuwa domin tsira da rayukansu.

A nasu bangaren jami’an ‘yan sanda sun yi gaggawar shiga tsakani domin a maido da doka da oda, amma abin mamaki sai ‘yan kungiyar suka yi musayar wuta da ‘yan sandan.

Adeola ya bayyana cewa an kashe mutane biyu tare da jikkata wasu mazauna yankin.

Crime Channel

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *