Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu
A matsayinmu na shugabannin kungiyar Gauta Club, mun saurari bayanai na bayan taro da aka gudanar tsakanin jami’an Gwamnatin Jihar Kano da kuma shuwagabannin kafafen yad’a labarai dake gudanar da shirye-shiryensu a Jihar Kano.
Mun yi nazari da duba na tsanaki akan matakan da wannan taro ya bijiro da su.
Don haka, a madadin shugabanni da ‘ya ‘yan wannan kungiya mai albarka ta Gauta Club wadda hadaka ce ta masu gwagwarmayar siyasa a kafafen yad’a labaru daga jam’iyyu daban-daban a Jihar Kano, muna jaddada goyon bayan mu dangane da matakan da masu ruwa da tsaki suka dauka domin tsabtace shirye-shiryen siyasa a kafafen yad’a labarai dake yad’a shirye-shiryensu a Jihar Kano.
Tun daga lokacin da aka fara daukar wannan mataki na gyara a inda shugabanin kafafen yada labarai wadanda suka hada da gidajen Radiyo da talbijin suka bayyana a satin da ya gabata, an fara samun gagarimin ci gaba.
Dakatar da gabatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye da nufin kawo karshen matsalolin da hakan yake haifarwa wanda ya haɗa da cin zarafin masu mutunci, yin kazafi da yin kalamai na ‘batanci da basu dace ba, abu ne da muke goyon bayansa, kuma za mu taimaka wajen samun nasarar wannan mataki.
Wannan mataki da masu ruwa da tsaki suka ɗauka ya yi dai dai, domin hakan zai kiyaye mutuncin mutane musamman shugabanni. Matakin kuma zai taimaka wajen kare kafafen yaɗa labarai daga fadawa cikin rikici da hukumomin dake sa ido a kan ayyukansu.
Hasali ma wannan mataki zai ƙara kare waɗanda suke yin hirar daga jefa kansu cikin laifi kamar yadda tanade-tanaden yada labarai ta tanada.
Wannan mataki zai taimaka wajen kare kima da martaba na addinin al’umma da kuma kyawawan al’adunmu da suka had’a da kara, yakana, jin kunya, ganin girman na gaba da sauran kyawawan halayen da aka san mu dasu.
Kididdiga da Hukumomin dake kula da yaɗa labarai suka fitar na nuni da cewa, Jihar Kano ce a kan gaba wajen sabawa ka’idoji da tanade-tanaden aikin jarida a fannin shirye-shiryen siyasa.
Wannan abin takaici ne, don haka daukar matakan doka da na aikin Jarida ya zama dole domin kare martabar jiharmu da kuma barwa na bayanmu kyawawan misalai.
A gaskiya babu wata al’umma da ta san ciwon kanta za ta zuba ido a na yi wa, jama’arta musamman shugabanni da martabar addininta da al’adunta Karan tsaye kuma ta kyale haka ya ci gaba.
A saboda haka ne mu kai maraba da wannan mataki na shugabannin kafafen yada labarai na dakatar da shirye-shiryen siyasa kai tsaye, domin hakan zai taimaka wajen tsabtace harshe da kiyayewa wajen cin zarafin masu mutunci. Wannan mataki ya yi dai dai da muradi, da bukatun al”ummar jihar Kano, don haka abin a yaba ne.
A bangarenmu na masu gwagwarmaya a Radiyo da gidajen talbijin, muna nuna cikakken goyon bayan mu tare da yabawa wannan mataki kuma zamu ci gaba da bada goyon bayan ga duk wani matataki na gyara a kowane mataki domin samun kyautatuwar al’amura.



Mun gode.
Sa hannun
Shugaban GAUTA CLUB
Alh Hamisu Danwawu Fagge
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD