Edu ya ce “A yau Majalisar ta amince da kafa asusun tallafawa jin kai da fatara da talauci wanda zai kasance karkashin hukumar gudanarwar Kwamitin
Alfijir Labarai ta rawaito Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin kafa Asusun tallafawa Jama’a don kawar da Talauci da za a rika fitar da dala Biliyan 5 duk shekara domin tafiyar da shirin.
Amincewa da kudurin kafa Asusun na zuwa ne a taron Majalisar zartarwa ta Tarayya da Shugaba Bola Tinubu ya Jagoranta a ranar Litinin a fadar Shugaban.
A cewar Ministar harkokin jin ƙai da rage radadin talauci Dakta Betta Edu, kuɗaɗen za su taimaka sosai wajen fuskantar duk wani yanayi na gaggawa a kasar.
Ministan Kuɗi da Haɗin Kan Tattalin Arziki Wale Edun da sauran Ministoci sun kasance tare da su a cikin hukumar don sauƙaƙe ayyukanta na Musamman na tara kuɗaɗe daga ƙungiyoyi masu ba da tallafi.
Edu ya ce “A yau Majalisar ta amince da kafa asusun tallafawa jin kai da fatara da talauci wanda zai kasance karkashin hukumar gudanarwar Kwamitin, sannan kuma ba shakka Mambobin kwamitin za su yi aiki da shi a tsanake wajen aiwatar da wannan asusun na jin kai da fatara.
Tabbas zai haɗa da Ministan Kuɗi da Haɗin Kan Tattalin Arziki ciki har da sauran Ministocin da suka dace da tsarin.
Wannan wani nau’i ne mai sassaucin ra’ayi na samar da kuɗaɗe, wanda ya kamata ya taimaka wa Najeriya yadda ya dace don magance rikice-rikice da kalubale da kuma magance matsalar talauci a Najeriya yadda ya kamata.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/KpTjEvHUjd3CVzIQp8CSkZ