“Akwai masu bayar da magani da su ka san abun da su ke yi, kuma sun iya gano ciwo, sun kuma san maganinsa, amma akwai masu bayar da magani na jabu, ‘yan bige masu bayar da magani daban ciwo daban,”
Alfijir Labarai ta rawaito babban malamin addinin Muslunci kuma shugaban majalisar Malamai ta ƙasa Sheikh Ibrahim Khalil, ya ce yin amfani da maganin gargajiya na samar da waraka fiye da sauran magunguna idan an yi amfani da shi yadda ya dace.

Malamin ya bayyana haka ne, a wajen taron kaddamar da tallafin bayar da magani ga marasa lafiya 500 da cibiyar kiwon lafiya ta Dr. Mamman Islamic Health Centre Ɗorayi dake Garejin Kamilu ta shirya domin murnar shigowar watan Rabi’ul Auwal.
Sheikh Ibrahim Khalil ya ce, samun kwararrun masu bayar da maganin gargajiya, zai taimaka wajen samun waraka ga marasa lafiya,
“Akwai masu bayar da magani da su ka san abun da su ke yi, kuma sun iya gano ciwo, sun kuma san maganinsa, amma akwai masu bayar da magani na jabu, ‘yan bige masu bayar da magani daban ciwo daban,”
“Ya na da kyau jami’o’in Najeriya su haɗa ilimin magajin gargajiya da na zamani waje ɗaya, domin samar da magunguna masu inganci da za su taimaka wa marasa lafiya, kuma magajin gargajiya shi ne kaɗai za ka sha ba tare da ya bar maka wata matsala ba a jiki (side effect) amma sai an sha shi bisa ka’ida.”
A ƙarshe Malam Khalil ya yabawa Dr. Mamam Islamic Health Centre Ɗorayi, bisa shiryar wannan gangamin bayar da magunguna kyauta ga marasa lafiyar 500.
A na nasa jawabin shugaban cibiyar Dr. Mamman Islamic Health Centre, Aminu Adamu wanda ake kira Dakta Mamman, ya ce sun shirya wannan gangami ne domin taimakawa masara lafiya masu fama da cututtukan da ke da wahalar jinya, da ma sauran cututtuka sanannu.
“Mutane 500 za mu duba, gwaji, da magani, duk kyauta ne komai girman lalurar, kawai abun da ake bukata wajen mara lafiya, ya yanki kati akan ₦1,000. Mun fara aikin a yau Asabar 1 da kuma gobe Lahadi 2 ga watan Rabi’ul Auwal 1445AH wanda ya yi daidai da 16 da 17 ga watan Satumba 2023.
“Zuwa wannan lokacin mun kusan ƙarar da rabin magungunan, saboda wasu tun asubahi su ka zo nan, kuma har yanzu wasu na ƙara shigowa, wasu ma sai zuwa gobe za su ƙaraso domin sun yi mana waya su na tahowa daga nesa, don haka za mu yi aikin har zuwa dare, idan kuma jama’ar ba su ƙare ba, za mu duba yiyuwar mu sake zama a ranakun Litinin da Talata.”

“Mun kashe kuɗi kusan miliyan da rabi don samar da magungunan, dole mu godewa jama’a da su ka taimaka mana da kuɗi, da abokan sana’a da su ba tallafama da magunguna, da waɗanda su ka kawo abinci, godiya ga kafafen yaɗa labarai da su ka taimaka mana wajen yaɗawa al’umma wannan shiri, kuma gashi sun amsa kira sun zo su na cin gajiyarsa.
Wasu daga cikin waɗanda su ka amfana da tallafin maganin sun bayyana farin cikinsu tare da godiya ga Dr. Mamman Islamic Health Centre Ɗorayi Garejin Kamilu bisa taimakon da ta ba su.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb