Kwankwaso Da Abba Sun Jagoranci Auren Gatan Mutum 1,800 A Kano

FB IMG 1697218100005

Gwamnatin Jihar Kano Karkashin jagorancin, Abba Kabir Yusif ta kaddamar da auren zawarawa 1,800 wanda aka gudanar a Babban Masallacin Juma’a na Gidan Sarkin Kano.

Alfijir Labarai ta rawaito Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Mataimakin sa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo da sauran jiga-jigan jam’iyyar ne, suka jagoranci daurin auren yar Gata da aka gudanar a yau juma a a Kano.

Haka zalika, an daura auren sauran zawarawan a kananan hukumomin Jihar Kano 44, wanda aka gudanar a masallatan Juma’a na shelkwatar kananan hukumomin, kamar yadda aka tsara.

Da yake Karin haske jim kadan da daura auren zawarawan karamar hukumar Kunchi, babban limamin karamar hukumar Kunchi, Imam Gwani Nazifi Abubakar, ya taya angwaye da amaren murnar sannan ya bukace su da su zauna da juna cikin aminci da amana

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *