Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Usaini Gumel, ya bayar da umarnin kamo wani Sufeto da aka zargi da nuna rashin kwarewa inda har kai ga hallaka wani mutum daya tare da jikkata wasu mutane biyu a jihar.
Alfijir labarai ta rawaito sanarwa da SP Abdullahi Haruna Kiyawa mai magana da yawun rundunar ya fitar a ranar Laraba, ta ce rundunar ‘yan sanda na bin diddigin lamarin da ya faru a unguwar Kurna, karamar hukumar Fagge jihar Kano a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2023 inda wasu gungun matasa suka fafata da wani sifeton ‘yan sanda. wanda bai samu wani umurni daga rundunar ‘yan sandan ba ya harba bindigarsa, kuma abin takaicin shi ne ya raunata wasu mutane biyu tare da hallaka wani mutum guda .
Sanarwar ta kara da cewa, a halin yanzu kwamishinan ‘yan sanda, CP Mohammed Usaini Gumel, FIPMA, psc, ya umurci kwamandan yankin Dala, ACP Nuhu Mohammed Digi da ya kamo sufeton ‘yan sandan domin gudanar da bincike kan lamarin don daukar matakan da suka dace akan shi.
Sanarwar ta yi Allah wadai da abun da sufeton yan sandan ya gudanar, Inda sanarwar tace kwamishinan yan sandan Kano ya himmatu tun da ya kama aiki a kano, don ganin yan sanda suna gudanar da aikin su bisa kwarewa da sanin makamar aiki.
Kwamishanan ‘yan sandan ya mika ta’aziyyasa ga iyalan mamacin da addu’ar Allah ya jikansa, ya bukaci jama’a da su kwantar da hankulan su domin rundunar ta dauki lamarin da matukar muhimmanci tare da tabbatar da adalci da gaskiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp