Farfesa Jega Ya Caccaki Kotun Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin Zaɓen Gwamnan Kano

FB IMG 1701269748995

Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega ya buƙaci a gudanar da bincike kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke kan rikicin zaɓen gwamnan Kano.

Alfijir labarai ta rawaito cewa kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja a ranar 17 ga Nuwamba, 2023 ta soke zaɓen gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP tare da bayyana abokin hamayyarsa Nasiru Gawuna na jam’iyyar adawa ta APC a matsayin wanda yayi nasara.

Amma a cikin kundin bayanan hukuncin da kotun da aka fitar kwanaki hudu bayan yanke hukuncin, ta bayyana Abba Kabir Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaɓen a karshen takardar.

Jaridar ta rawaito cewa fitar takardar hukuncin ta haifar da ruɗani tare da gudanar da zanga-zangar adawa da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara a Kano.

Da yake magana a gidan Talabijin na Channels TV’s ta cikin shirin Politics Today, a ranar Litinin, Farfesa Jega ya bayyana hukuncin kotun ɗaukaka ƙara na Kano da ke cin karo da juna a matsayin “abin takaici ne matuƙa.”

“Babu shakka… wannan sabon lamari da ya faru game da lamarin a Kano abin takaici ne. Baya ga Chidi Odinkalu, na ji kuma na karanta yadda manyan lauyoyi da yawa a Najeriya suna ƙalubalantar abinda ya faru.”

“Za ku yi tsammanin kotuna musamman a matakin ɗaukaka ƙara zasu yi irin wannan abun? Amma abin gaskiya abin mamaki ne.” Ina ji shi

A cewarsa “Yanayin da aka bayar a matsayin rubutaccen hukuncin ya saɓa wa wanda aka karanta a cikin kotun, tabbas hakan abin mamaki ne kuma abin takaici ne matuƙa.

“Na yarda, ni ba lauya ba ne, amma na yarda cewa akwai buƙatar a yi cikakken bincike akan wannan abu.” In ji Jega

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *