Alfijr ta rawaito Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Ogun, Frank Mba, a ranar Juma’a ya nuna cewa zai binciki zargin yunkurin Gwamna Dapo Abiodun zuwa wasu rumfunan zabe yayin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki da za a yi ranar Asabar a jihar.

Aminiya ta ruwaito cewa, an samu bacin rai a ranar Asabar da ta gabata, yayin da Abiodun ya zagaya wasu rumfunan zabe a Iperu-Remo, ciki har da inda abokin hamayyarsa, kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Ladi Adebutu, ya kada kuri’a.

Abiodun da Adebutu sun fito daga yankin Iperu-Remo, kuma rumfunan zaben su ba su da nisa tsakaninsu.
Wakilinmu ya lura cewa, bayan kada kuri’a a rumfar zaben an ga gwamnan ya je rumfar zabe daban-daban domin sa ido kan yadda zaben ke gudana.
Abiodun ya yi zabe a Ward 3, Unit 002, Osanyin Iperu, karamar hukumar Ikenne ta jihar.

Adebutu ya bayyana matakin na Abiodun a matsayin cin zarafin dokar zabe.
Ya ce, “Abin takaici ne wadanda za su jagoranta su ci gaba yin shiririta.
Mun ga gwamnan jihar yana zagayawa a duk fadin wannan yanki, daga wannan rumbun zabe zuwa waccan har ma da raba takardar dala.
Ba za a iya yin zabe cikin gaskiya da adalci ba.”

Sai dai mai ba gwamna Abiodun shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Remmy Hazzan ya bayyana zargin da cewa ba gaskiya ba ne, kuma shifcin Gizo ne.
Hazzan ya ce “rashin tunanin dan takarar gwamna na PDP ne a jihar a ce gwamnan yana raba daloli”
A ranar Juma’ar da ta gabata yayin wani zama na tattaunawa tsakanin jami’an tsaro da ‘yan takarar jam’iyyun siyasa gabanin zaben gwamna a Abeokuta, Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Sikirullahi Ogundele, ya nuna damuwarsa da cewa matakin Abiodun ya saba wa dokar zabe, amma duk da haka ‘yan sanda sun kauracewa sa ido.
Da yake mayar da martani kan zargin, CP Mba ya ce bai san da faruwar lamarin ba, amma ya sha alwashin binciki lamarin.
“Akan yunkurin da ake zargin gwamnan ya yi a rumfar zabe a ranar zabe, gaskiya, na fada muku, wannan ne karo na farko da na ji hakan.
“Zan bincika, zan gano ko da gaske ne ya faru.
Idan ya faru, zan yi duk abin da ya dace don tabbatar da cewa hakan bai sake faruwa ba.
“Kuma ina so in gargadi sauran jiga-jigan siyasa, ba zan bar kowa ya zagaya a ranar zabe ba,” in ji MBA.
A Karshe ya tabbatar wa jam’iyyu cewa jami’an tsaro “za su yi adalci tare da aiwatar da doka cikin adalci da daidaito” a lokacin zabe mai zuwa.
Daily Trust
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇