Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau
Alfijr ta rawaito wani Jigon a jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Sani Abdullahi Wamban Shinkafi, ya ja hankalin shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya kuskura yace zai sanya kafa ya shure umurnin da kotu ta bayar na aci gaba da amfani da tsaffin kudi daga yanzu har zuwa 31 ga wata 12 na shekara ta 2023, don haka ya mutunta umurnin kotu.

Wamban shinkafi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a gidansa da ke Gusau a ranar juma’a, ya ce, dole ne shugaba Buhari ya mutunta hukuncin da kotun koli ta yanke, sannan ya bar sabbi da tsofaffin takardar Naira su dawo suna aiki a lokaci guda har zuwa ranar 31 ga watan Sha biyu na wannan shekara.

Ya Kara da cewa“Tunda kotun koli ta yanke hukuncin cewa tsohon Naira da sabon Naira su ci gaba da zama bisa doka, babu wani mutum a kasar nan komai girmansa ya karya wannan doka.
Sani ya ce”Ina kira ga shugaban kasa da ya mutunta umarnin kotu sannan kuma ya umarci Babban Bankin kasa ( CBN) da ta saki kudaden a wurare dabam-dabam da ya dace”.in ji shi

Shinkafi ya bayyana cewa, sauya launin wadan nan ta kardun kudi na Naira ya jefa ‘yan Najeriya da dama cikin halin kuncin rayuwa , a cewarsa Buhari bai samu shawara na gari ba daga gwamnan babban bankin kasar, Mista Emeifele yana mai jaddada cewa, “ba haka kasashe masu ci gaba ke canza kudadensu ba”.
Ya ce “An samu canjin kudade a kasashe irin su Amurka da Saudi Arabia da sauran kasashe masu ci gaba amma ba su hana amfani da tsofaffin takardun kudi ba a lokaci guda”.
Wamban shinkafi ya yabawa gwamnonin jihohin Zamfara da Kaduna da Kogi bisa gagarumin kokarin da suke yi na ceto kasar nan daga durkushewa baki daya sakamakon tabarbarewar kudi, ya Kuma Bukaci gwamnonin da su koma kotu idan shugaba Buhari, AGF da CBN suka ki yin aiki kamar yadda kotun koli ta umarta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux