Kotun Zabe Ta Tsige Sanatoci 5 Ƴan Majalisar Wakilai 25 Na APC PDP LP da NNPP kwanaki 100

Yawancin ‘yan Majalisun da suka yi rashin nasara a Kotu na jam’iyyun APC, PDP, LP da NNPP sun lashi takobin ɗaukaka ƙara.

Alfijir Labarai ta rawaito Jam’iyyar APC ce ta fi kowace jam’iyya rasa Sanatoci yayin da kuma ita ce ta fi amfana da hukuncin kwace kujerun mambobin majalisar wakilai zuwa yanzu a kotun kararrakin zabe.

PDP ta rasa kujerun yan majalisar wakilai 12, Labour Party ta rasa 10 yayin da APC da NNPP suka rasa ɗai ɗai.

Akalla mambobin majalisar wakilan tarayya 25 da Sanatoci 5 suka rasa kujerunsu kawo yanzu a Kotun sauraron ƙorafe-korafen zaɓe a faɗin Najeriya.

Yayin da jam’iyyar APC ce kan gaba wajen rasa kujerun Sanatoci a hukuncin da Kotu ta yanke, a ɗaya bangaren kuma ita ta fi amfana da hukuncin kwace kujerun mambobin majalisar wakilai.

Wannan ta faru ne duk a cikin kwanaki 100 bayan magatakardan majalisar dattawa da na Majalisar Wakilan Tarayya sun rantsar da majalisa ta 10.

Yawancin ‘yan Majalisun da suka yi rashin nasara a Kotu na jam’iyyun APC, PDP, LP da NNPP sun lashi takobin ɗaukaka ƙara.

Sanatocin da APC da PDP suka rasa zuwa yau A mazaɓar Sanatan Kogi ta gabas da na Kogi ta tsakiya, Kotun zaɓe ta soke nasarar jam’iyyar APC mai mulki.

Haka nan kuma jam’iyyar APC ta sake rashin nasara a Kotu, inda aka rushe nasarar Sanatocinta a mazaɓar Delta ta tsakiya da kuma Delta ta kudu.

Bayan haka Kotun zaɓe ta rushe nasarar jam’iyyar PDP a mazaɓar Sanatan jihar Filato ta kudu.

Jerin jihohin da za a gudanar cikon zaɓe, wanda kotun ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta shirya ƙarashen zabe a mazaɓar Delta ta tsakiya, Delta ta kudu da Kogi ta gabas cikin kwanaki 90 masu zuwa.

A ɗaya bangaren, Kotun ta tsige mambobin majalisar wakilan tarayya 26 zuwa yanzu, sai dai Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta maida ɗaya daga cikinsu.

Jam’iyyar PDP ta rasa mambobin majalisar wakilai 12 yayin da Labour Party ta rasa guda 10.

Jam’iyyar APC da kuma NNPP sun rasa ɗai-ɗai su kuma.

Hakazalika Kotu Ta Tsige Dan Majalisar PDP, Ta Tabbatar da Nasarar ‘Yan Takarar APC 2 a Taraba.

Sai kuma yanzu haka mun kasa mun tsare muna sauraren yadda zata kasance a kotun sauraren kararrakin zaben a kurejar geamnan kano.

Sai a kasance da Alfijir Labarai domin jin yadda zata kasance.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *