Wani matashi ya mutu a kokarinsa na dauko wasu zannuwan da suka fada rijiya a Kano

Saminu ya ci gaba da cewa, an nemi Ayuba da ya taimaka wajen dauko wasu kaya da suka fada cikin rijiya.

Alfijir Labarai ta rawaito wani matashi dan shekara 37 mai suna Umar Ayuba ya rasu a wata rijiya da ke Kawon Maigari a karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a Kano.

Saminu ya bayyana faruwar lamarin ne da yammacin ranar Talata.

“Mun sami kiran gaggawa da misalin karfe 5:20 na yamma. daga wani Mamuda Abdallah ya ce wani mutum ya makale a cikin rijiya.

“Nan da nan muka aika da tawagar jami anmu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 5:32 na yamma,” in ji shi.

An nemi Ayuba da ya taimaka wajen ceto wasu mata da suka fada cikin Rijiyar ne. In Ji Saminu.

A cewarsa, wanda abin ya shafa ya shake a ciki saboda rashin iska.

“An fito da shi daga rijiyar a sume aka mika shi ga Insp. Adamu Sani na rundunar ‘yan sanda ta Hotoro,”

Insp ne ya jagoranci kai mutumin zuwa Asibitin kwararru na Murtala Muhammed, bayan da likita da ke bakin aiki ya dubu shi nan ya tabbatar da mutuwarsa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *