Kotun Koli Ta Ɗage Sauraren Karar Musayar Naira Domin Yanke Hukunci

Alfijr ta rawaito Kotun koli ta dage sauraren karar da wasu gwamnatocin jihohi suka shigar kan manufar musanya Naira na babban bankin Najeriya.

Kotun kolin ta dage sauraron karar a ranar Laraba bayan ta saurari bahasi da lauyoyin da ke kare jam’iyyun.

Gwamnonin Jihohin kasar dai sun maka babban lauyan gwamnatin tarayya kara kotu kan wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairun 2023 da gwamnatin tarayya ta kayyade domin musanya daga tsoho zuwa sabon Naira.

Bayanan da abin ya shafa sun hada da N200, N500 da kuma N1,000.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce tsohon N200 ya kamata ya ci gaba da zama na doka tare da sabbin N200, N500 da N1,000.

Bayan sauraron dukkan bangarorin da ke kara a ranar Laraba, Kotun Koli ta sanya ranar 3 ga Maris don yanke hukunci.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *