Alfijr ta rawaito Babban kotun shari’ar musulunci da ke zaman ta a Post office, karkashin mai shari’ah, Salisu Ibrahim Koki, ta kara jaddada umarnin ta na kamun tsohon shugaban karamar hukumar Kumbotso Kabiru Ado Panshekara.

Hakan ya biyo bayan karar sa da wani Dan kasuwa a jihar Kano Alhaji Auwalu ya shigar Akansa.
Alhaji Auwal ya yi karar tsohon Chairman din kan zargin, ya sayar masa da wani katon fili da ake yin kamfani a ciki a yankin Challawa, sai dai daga baya wanda aka siyarwar, ya gano akwai matsala akan fili, dan haka ya bukaci a dawo masa da kudin sa.
Tun da ya dawo da miliyan 20 sai yake ta yi masa jeka dawo akan sauran kudin, hakan tasa ya yi karar sa, kasancewar bai halarci zaman kotun ba, ta yi umarnin a kamo shi har sau biyu.
Lauyan tsohon shugaban karamar hukumar ta Kumbotso, ya roki kotun da ta je ta gano gidajen sa guda biyu daya Sharada, daya kuma a Kabuga housing estate, da kuma wata gona a Challawa, sannna a sa masa ranar biyan kudin idan bai biya ba, a sayar da daya daga ciki tun da dukkan su sun kai kudin da ake bin sa, kuma ya roki kotun da ta janye umarnin kamun a zaman da akayi a ranar Laraba.
Mai shari’a ya amshi wasu batun na gano wuraren amma ba ta amsa batun janye umarnin kamun ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇