Alfijr ta rawaito Mai shari’a Amina Adamu da ke babar Kotu mai lamba 9 a jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan da ta kama wani tsohon daracta a hukumar Hisbah Dayyabu Muhammad da laifin kashe bazawarsa mai suna Hauwa.
Laifin kisan ya saba doka, ta kundin Pinal Code sashe na 221.
Bincike ya tabbatar da Dayyabu almajiri ne a gidansu Marigayiyar Hauwa, kuma jami’i ne na Hisbah wanda ya nuna sha’awarsa ta auren Hauwa, daga nan suka kulla soyayya.
Yayin da Dayyabu ya zo da maganar aure, iyayen Hauwa sun ce ba za su bashi ita ba saboda suna ganin akwai tangarda a tarbiyyarsa, wannan yasa Hauwa daga baya ta sauya ra’ayi a kansa, tace bata yi.
Wannan lamari dai ya fusata Dayyabu, in da ya zo har gida a shekarar 2011 har daki ya nemi ganin Hauwa.
Bai kasa a guiwa ba nan ya dauko wuka ya caccaka mata a jikinta, kuma wannan dai shi ne sanadin mutuwarta.
Bayan samun gamsassun hujjoji, mai shair’a Amina Adamu ta ce ta gamsu da komai da aka gabatar na hujja, don haka ta yanke masa hukunci ta hanyar rataya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
You might like
Previous PostNext Post
Mafi shahara
‘
Ta faru ta kare: Matasa sun yi wa shugaban APC tsirara bayan sun lakada mashi duka a Nasarawa
byIsyaku Garba-December 10, 2022
December 11, 2022
Saurayi ya yi wa mahaifiyarsa mai shekara 70 dukan tsiya (Bidiyo)
December 14, 2022
Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke tsakanin garuruwa biyu a Najeriya, an rasa rayuka
December 11, 2022
Siyasa
Rukunin labarai
Adadin mabiya
8597934
Sanarwa
Seniora Tech tana N0.50 Taushi Plaza, Bello way Birnin kebbi. Ita ke tafiyar da shafukan isyaku.com da Seniora News a karkashin kampanin Seniora Int’l Ltd RC 1470216
ABOUT US
Lorem Ipsum is simply dummy text of the printing and typesetting industry. Lorem Ipsum has been the industry’s.
Copyright © 2022 ISYAKU.COM
Our website uses cookies to improve your experience. Learn more