Kotu Ta Yankewa Shahararun Yan TikTok Ɗin Nan Hukunci

Alfijr ta rawaito kotun shari’ar musulunci da ke zamanto a Kano ta sako Murja Ibrahim Kunya tare da Ashiru Idris Mai-Wushirya, bayan zaman gidan yari na sama da makonni biyu.

Sai dai kotun ta kafa sharadin cewar Murja Kunya za ta yi sharar asibitin Murtala har tsawon makonni uku, sannan za ta dauki tsawon watanni shida tana ziyartar hukumar Hisbah ta Kano.

Haka zalika kotun takuma ce, Mai-Wushirya, BBC, da kuma Sadik Shariff an umarce su da su yi sharar masallacin Murtala na tsawon makonni uku.

Idan zaku iya tunawa, zauren malaman Kano ne ya gurfanar da matasan gaban kotu, bisa zarginsu da wallafa kalaman batsa a dandalin TikTok.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *