Alfijr ta rawaito Jami’ar Maryam Abacha (MAAUN) da ke Kano, ta sanyawa sashin Kimiyyar Kiwon Lafiya na Jami’ar sunan fitaccen Ɗan kasuwa kuma dattijo, Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

An kaddamar da ginin ne a ranar Alhamis, 2 ga Maris, 2023, wanda Dokta Munzali Aminu Dantata, wanda ya wakilce mahaifin nasa a wajen bikin bude sashin.

Tun da farko, wanda ya kafa kuma shugaban majalisar gudanarwa ta MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya ce jami’ar ta yanke shawarar sanya wa ginin sunan dattijon jihar Kano ne, saboda sadaukar da kai da kuma gudunmawar da ya bayar wajen habaka tattalin arzikin jihar Kano da Najeriya baki daya.

Farfesa Gwarzo wanda ya bayyana Alhaji Aminu Dantata a matsayin babban mai taimakon al’umma, ya kuma roki Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da ba shi karfi da lafiya ya ba shi damar ci gaba da yi wa al’umma hidima.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇