Kotu Ta Yanke Masa Hukuncin Rataya Bayan Kashe Kishiyar Mahaifiyarsa A Kano

Alfijr ta rawaito Babbar kotun mai zaman ta a sakatariyar Audu Bako a Jihar Kano, ƙarƙashin Mai Shari’a Aisha Mahmud, ta yanke wa wani matashi, Sagiru Wada hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe kishiyar mahaifiyarsa.

A yayin yanke hukuncin a jiya Laraba,

Mai Shari’a da take yanke hukuncin a ranar Laraba, ta yi karatun baya, in da ta samu matashin da laifin daddatsa kishiyar mahaifiyarsa da adda.

Bisa wannan dalili ta yanke masa hukuncin kisa, karkashin sashi na 221 na kundin dokar laifuka na Kano.

Mai shari’a ta ce ta gamsu da tuhumar da ake masa bayan samun cikakkun shaidu, ta kuma yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An gurfanar da mai katobarar Wada ne, bisa laifin kashe kishiyar mahaifiyarsa, Zainab Dan-Azumi da wata adda shekaru 8 da suka gabata.

Barista Rabi’u Abubakar shine mai kare wanda ake tuhuma, ya shaida wa kotun cewa matashin bashi da lafiyar ƙwaƙwalwa, amma kotun tai watsi da wannan rokon bisa cikakkun shaidu da tayi amfani da su bisa hangenta.

Barista Tijjani Ibrahim wanda shine ke kare wadda aka kashe ya ce, kotu ta yi nazari ta ga babu wani dalili da za a ce yana da Ciwon hauka a ƙwaƙwalwar sa.

Ya kara da cewa hakan bai gamsar da kotu ba, inda ta yi watsi da rokon tayi abin da ya kamata.

A nasa bangaren lauyan wanda ake ƙara ya ce za su zauna su yi nazari kan mataki na gaba da za su ɗauka na gaba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *