Kotu ta janye belin da aka baiwa tsohon Akanta-Janar na ƙasa, Ahmed Idris

📸Ahmed Idris

Mai shari’a Yusuf Halilu na babbar kotun babban birnin tarayya Abuja a Maitama, a yau Talata ya soke belin tsohon Akanta-Janar na Ƙasa, Ahmed Idris da daya daga cikin wadanda ake tuhuma a shari’ar da ake yi masa bisa zargin karkatar da kudaden jama’a har Naira biliyan N109.5.

Alfijir Labarai ta rawaito alkalin kotun ya soke belin daya wanda ake tuhuma, Geoffrey Olusegun Akindele, biyo bayan rashin bayyanarsa a kotu domin ci gaba da shari’ar.

Akindele, wanda shi ne wanda ake tuhuma na biyu a shari’ar mai lamba CR/199/2022, da kuma Idris suna fuskantar tuhume-tuhume tare da Mohammed Kudu Usman da Kasuwar Musayar Kayayyaki da ke Gezawa.

Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, ta maka su kara ne a gaban kotu kan tuhume-tuhume 14 da suka hada da sata, da almundahana da dukiyar al’umma zuwa Naira biliyan 109.5.

EFCC ta yi zargin cewa ta haka ne suka aikata laifin da ya saba wa sashe na 155 na dokar Penal Code Act Cap 533 na Dokokin Tarayyar Najeriya na 1990 da kuma hukunta su a karkashin wannan sashe.

A ci gaba da sauraron karar a yau Talata, Mista Akindele bai halarci kotun ba har zuwa lokacin da ake sauraron karar, duk da cewa Idris da Usman suna gaban kotun.

Duk da rokon da lauyan Mista Akindele, S.E. Adino ya yi na cewa wanda yake karewa yana kan hanyar zuwa kotu, inda ya gabatar da cewa shi (Akindele) yana kasancewa a kotu ko da yaushe domin fuskantar shari’a, Mai shari’a Halilu ya dage kan soke belin wanda ake kara na biyu.

Daga nan sai ya dage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar 1 ga watan Fabrairun 2024.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *