Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke hukuncin cewa hukumar kiyaye hadurra ta ƙasa FRSC ba ta da hurumin gudanar da ayyukanta a kan hanyoyin jiha da na ƙananan hukumomi. Law Enforcement
Kotun ta kuma bayyana cewa matakan da jami’an FRSC ke ɗauka a cikin birnin Kano ba bisa ƙa’ida bane, kuma suna take haƙƙin al’umma.
Yayin da ya ke yanke hukunci a ranar Alhamis kan ƙarar da lauya Abba Hikima, ya shigar a kan FRSC, mai shari’a M. S. Shuaibu ya ce jami’an hukumar sun wuce iyakokin ikon da doka ta basu.
Kotun ta bayyana cewa irin wannan mataki ya saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999, musamman sashe na 35 da na 41, waɗanda su ka tanadi haƙƙin ƴancin kai da kuma yancin zirga-zirga. Maps
Kotun ta amince da duk manyan buƙatun da mai karar ya gabatar, ciki har da bayar da umarnin haramta wa jami’an FRSC ci gaba da tsayar da direbobi ko muzgunawa masu amfani da hanyoyin jihar Kano ba tare da cikakken ikon doka ba.
Haka kuma kotun ta umurci FRSC da ta wallafa nemi afuwa ga jama’a a wata jaridar ƙasa, tare da biyan mai ƙarar diyyar Naira 800,000 a matsayin diyya da kuɗin shari’a. Famous Quotations
Lamarin ya samo asali ne a watan Yulin shekarar da ta gabata, lokacin da jami’an FRSC suka kafa shingayen bincike a hanyoyin cikin birnin Kano, inda su ka riƙa tsayar da direbobi, ciki har da Abba Hikima, suna neman lasisin tuƙi tare da yi musu tambayoyi ba tare da sun aikata wani laifin karya dokar hanya ba.
Daga nan ne Hikima ya garzaya babbar kotun tarayya domin ƙalubalantar abin da ya bayyana a matsayin take haƙƙinsa.
A cewarsa, ikon da dokar FRSC ta tanada ya taƙaita ne ga manyan hanyoyin gwamnatin tarayya kawai, ba ya shafar hanyoyin jihohi ko na ƙananan hukumomi.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t
