Kotu ta ci tarar tsohon gwamnan Kaduna El Rufa’i miliyan 900, sakamakon take hakki

FB IMG 1748414134353

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta yanke hukuncin biyan diyyar naira miliyan 900 a kan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai, da wasu mutum biyar, sakamakon take hakkin dan adam da suka yi wa dattawan Adara daga Kudancin Kaduna.

Mai shari’a Hauwa’u Buhari ce ta yanke wannan hukunci a ranar Talata, 27 ga Mayu, 2025, a cikin ƙarar da Mista Awemi Maisamari tare da wasu dattawan Adara takwas suka shigar, bayan da aka tsare su ba bisa ka’ida ba a shekarar 2019.

Kotun ta bayyana cewa matakin da El-Rufai ya ɗauka na tsare wadannan dattawa ya sabawa doka, kuma ya tabbatar da cewa tsohon Gwamnan yana da alhakin biyan diyya bisa barnar da aka yi wa waɗanda lamarin ya shafa.

Mai shari’a Hauwa’u Buhari ta umarci El-Rufai ya biya Naira miliyan 900 a matsayin diyyar matakin da ya ɗauka da kansa na kama su ba tare da sahihin umarnin kotu ba.

Baya ga hakan, kotun ta kuma umarci Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Sufeton ‘Yan Sanda na Ƙasa, da kuma Kwamishinan ‘Yan Sanda na Kaduna su biya kowanne daga cikin waɗanda aka kama kudin naira miliyan 10 a matsayin diyya ta musamman.

Da take martani bayan yanke hukuncin, lauyar wadanda suka shigar da ƙarar, Gloria Ballason, wadda ta jagoranci fitattun lauyoyi irinsu Alkali da J.N. Buzun (SANs), ta bayyana hukuncin a matsayin wata nasara mai tarihi a yaƙi da cin zarafin ɗan adam da wulakanta ikon gwamnati.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *