Kotu ta bada umarnin mayar da sanata Natasha bakin aikinta

FB IMG 1751644958902

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta umarci Majalisar Dattijai da ta dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda aka dakatar.

Yayin yanke hukunci, Mai Shari’a Binta Nyako ta bayyana cewa dakatar da Natasha na tsawon watanni shida ya yi tsauri fiye da kima.

Kotun ta ce Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, bai yi kuskure ba lokacin da ya hana Natasha magana a zauren majalisa, saboda a lokacin ba ta zaune kan kujerar da aka ware mata ba. Sai dai kotun ta bukaci Natasha ta bai wa majalisar hakuri.

A cewar kotun, tun da majalisa tana da kwanaki 181 a kowanne zango, dakatar da Natasha tsawon watanni shida ya yi kama da hana mazaɓarta wakilci har na kusan kwanaki 180.

Kotun ta jaddada cewa duk da cewa majalisar na da ikon ladabtar da ɗan majalisa, bai kamata hukuncin ya kai ga hana ayyukan wakilci ba.

Mai shari’a Nyako ta kuma yi watsi da ƙarar Akpabio na cewa kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar.

Majalisar Dattawa ta dakatar da Natasha a watan Maris bayan ta zargi Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, da cin zarafi ta fuskar lalata.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *