Hukuncin ya tabbatar da zaben da ya bayyana Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 525,299 yayin da Yilwatda ya samu kuri’u 481,370.
Alfijir Labarai ta rawaito Kotun sauraren kararrakin zaben gwamna da ke zamanta a Jos a yankin Arewa ta tsakiya ta Najeriya ta amince da zaben gwamna Caleb Mutfwang na jam’iyyar PDP.

Kwamitin mai mutane uku, a cikin hukuncin da aka yanke ranar Juma’a, baki daya sun amince da cewa mai shigar da kara ya gaza a cikin karar da ta shigar saboda rashin cancantar.
Mai shari’a Sunday Olorundahunsi, da ke karanta hukuncin, ta yi watsi da duk wasu dalilai guda uku da mai shigar da kara kuma dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Nentawe Yilwatda ya zayyana.
A ranar 20 ga watan Maris, jami’in zabe na INEC a jihar, Farfesa Idris Amali, ya bayyana Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 525,299, yayin da Yilwatda ya samu kuri’u 481,370.
Sakamakon ya nuna cewa PDP ta samu nasara a kananan hukumomi 10 da suka hada da Barkin Ladi, Bassa, Lantang North, Langtang South, Riyom, Mikang, Mangu, Jos East, Qua’an Pan da Pokkos.
A daya bangaren kuma, APC ta samu kuri’u mafi yawa a kananan hukumomin Jos ta Gabas guda bakwai, Kanke, Kanam, Pankshin, Shendam, Wase, da Jos ta Arewa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb