Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta magantu kan wani rahoton da ke cewa jami’anta sun kama daya daga cikin alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano da ya yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar na 2023.
Alfijir Labarai ta rawaito biyo bayan zargin da wasu manyan jami’an gwamnatin Kano suka yi, inda suka bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ta yi imanin cewa jami’an tsaro sun tsorata da kama Alkalan da suka gudanar da hukuncin zaben ranar 18 ga watan Maris.
Da yake zantawa da PRNigeria ta wayar tarho, mai magana da yawun hukumar DSS, Dr. Peter Afunanya, ya musanta ikirarin na mai magana da yawun gwamnan Kano.
Afunanya ya ce: “Wannan magana ce mai ban dariya. Kame alkalai akan wane dalili? Ba gaskiya bane.”
Idan dai za a iya tunawa, yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan Talabijin na Channels, babban sakataren yada labaran ya ce, “babu dalilin da zai sa hukumar DSS za ta kama alkali ba tare da wata tuhuma ba.
Hukumar DSS ta kama daya daga cikin alkalan da suka yanke hukuncin a Kano, kuma na yi imanin cewa tsoratarwa ce.
“Hatta wannan hukunci na zahiri da suka zartar, ba mu san daga ina suka fitar da shi ba.
Watakila, sun yanke hukuncin ne a karkashin tilas duk da dai, ban tabbata ba.
Ba mu san inda suka yanke hukuncin ba kuma ba mu san halin da suke ciki ba saboda kawai muna iya ganin su a kan allo ne muma.
“Abubuwa da yawa sun faru a bayan fage, kuma abin mamaki ga wanda aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben bai ma shiga cikin lamarin ba.
Gawuna ya tsaya takara, ya amince da shan kaye, kuma ya taya Abba Kabir murna, ya ce ba zai je kotu ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb