Kotu Ta Aike Da Shugaban EFCC Bawa Gidan Gyaran Hali

Alfijr ta rawaito Babbar Kotun jihar Kogi ta ba da umarnin aikewa da Abdulrasheed Bawa Shugaban EFCC gidan gyaran hali saboda kin bin umarnin kotu.

Mai Shari’a R.O. Ayoola ne ya bayar da umarnin a zaman kotun na ranar Litinin din nan.

Kotun ta kuma umarci Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, da ya kama tare da tsare Abdulrasheed din a gidan gyaran hali na Kuje har na tsawo kwana 14, har sai ya kare kansa daga zargin rashin da’ar.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *