Gwamnatin Jihar Kano ta gode wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, saboda gaggawar ɗaukar matakin da su ka yi bayan kisan gillar mutane 16 ’yan asalin Kano a Udene, da ke ƙaramar hukumar Uromi ta Jihar Edo.
Gwamnan ya sake buƙatar a gudanar da shari’a ta gaskiya, tare da bayyana waɗanda aka kama a fili, domin tabbatar da cewa an yi adalci.
Gwamna Abba cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa-hannun Kwamishinan yaɗa labarai, Kwamared Ibrahim Waiya, ya yaba wa tawagar Gwamnatin Tarayya da Gwamnan Edo saboda ta’aziyyar da ya zo Kano, da kuma kudurin su na tabbatar da adalci ga waɗanda aka kashe.
Ya kuma yaba wa Gwamnan Edo saboda tattaunawa da al’ummar Hausawa a Jihar Edo da kuma alƙawarin biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu.
Haka kuma Gwamnan ya yaba Shugaba Tinubu bisa umarnin da ya bai wa hukumomin tsaro domin gano waɗanda ke da hannu a kisan, wanda ya bayyana hakan a matsayin ƙwazon da Gwamnatin Tarayya ta nuna wajen kare dukkan ’yan Najeriya.
Gwamnatin Jihar Kano ta kuma yi alƙawarin ci gaba da sa ido kan lamarin don tabbatar da adalci da biyan diyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD