Karancin Man Fetur: DSS Ta Fafata Da Dillalan Man Fetur, NUPRC A Kano

Alfijr ta rawaito hukumar DSS, ta Gayyaci Masu Kasuwar Man Fetur Na Nijeriya (IPMAN) , Nigeria Upstream wato hukumar kula da harkokin man fetur da sauran masu ruwa da tsaki, inda ta umurce su da su gaggauta magance matsalolin.

Taron, a cewar wani babban jami’in DSS, wanda baya son a ambaci sunansa, an yi shi ne a ranar Litinin da ta gabata, inda aka kwashe sa’o’i da dama a tsakanin jami’an tsaro, ‘yan kasuwar man fetur da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ce, ’yan kasuwa sun jagoranci hukumar DSS kan matsalolin da suke fuskanta da kuma yadda za a kai kayayyaki daga sassan Najeriya zuwa Kano.

A cewarsa, wasu daga cikin kalubalen da suke fuskanta sun hada da tsadar isar da man fetur ga wannan bangare na al’ummar kasar nan, rashin kyawawan hanyoyi da ke haifar da lalacewar tayoyinsu akai-akai, da kin biyansu kudaden Sufuri.

Hakazalika. Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, DPR ta riga ta kafa wata tawaga ta mutum uku da za ta sanya ido a kai a Kano, wadda za ta fara aiki a yau Talata domin tabbatar da wadatar da jama’ar Kano ba tare da katsewa ba.

Hukumar ta DPR, ta ce ta baiwa hukumar DSS tabbacin bin ka’idar samar da mai ba tare da katsewa ba wanda nan da ‘yan kwanaki masu zuwa za ta kubutar da Kano daga dogayen layukan masu ababen hawa a gidajen man.

Solacebase

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

2 Replies to “Karancin Man Fetur: DSS Ta Fafata Da Dillalan Man Fetur, NUPRC A Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *