Peter Obi Ya Caccaki Shugaba Tinubu Kan Rashin Iya Mulki

IMG 200618 22626 1782155193276

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa, yana mai cewa matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro da gazawar gwamnati sun kai matakin da ke buƙatar ɗaukar mataki a gwamnatance.

Obi ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X bayan sanarwar da Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, ya yi na shirin yin murabus.

Ya ce kamar yadda aka yi kira ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi murabus kafin zaɓen 2015 saboda matsalolin tsaro da tattalin arziki, haka ma ya kamata a riƙa ɗora shugabanni alhakin gazawar da ta faru a mulkinsu.

Obi ya tunatar da alkawuran da Tinubu ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023, musamman kan samar da wutar lantarki, yaƙi da cin hanci da inganta rayuwar al’umma.

A cewarsa, matsalolin tsaro, sace-sacen mutane, ƙarancin wutar lantarki da tsadar rayuwa sun ƙara ta’azzara a ƙasar, lamarin da ya nuna cewa gwamnati ta gaza cika alƙawuran da ta ɗauka.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce murabus ɗin shugaban ƙasa zai ƙarfafa al’adar ɗaukar alhaki a siyasa da kuma nuna cewa mukamin gwamnati amana ce, ba wata dama ta kashin kai ba.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *