Mayaƙan sa-kan za su taimaka wa sojojin Nijar a filin daga, kula da lafiya da sufuri da sauransu, idan buƙatar hakan ta taso.
Alfijir Labarai ta rawaito Gwamantin sojin Nijar ta fara ɗaukar mayakan sa-kai a shirinta na tunkarar dakarun kungiyar ECOWAS da ke shirin daukar matakin soji da nufin dawo da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar.
Matasa masu akalla shekaru 18 ne za a dauka a rundunar sa-kan mai suna VDN a taƙaice, inda ake tantance su a Filin Wasa na Janar Seyni Kountche da ke birnin Yamai da kuma iyakar ƙasar da Najeriya da Jamhuriyar Benin.
Mayaƙan sa-kan za su taimaka wa sojojin Nijar a filin daga, kula da lafiya da sufuri da sauransu, idan buƙatar hakan ta taso.
Burkina Faso tana rundunar sa-kai mai irin wannan suna, da ta kafa domin taimaka mata yaƙi da ta’ddancin da ke ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM