Bazoum “yana cike da karsashi” ko da yake har yanzu babu wutar lantarki a gidan da ake tsare da shi.
Tawagar Kungiyar ECOWAS karkashin jagorancin tsohon Shugaban Nijeriya Janar Abdulsalami Abubakar ta gana da hambararren shugaban Nijar Mohamed Bazoum a Yamai, babban birnin kasar ranar Asabar.
Wata majiya ta kusa da ECOWAS da ke cikin tawagar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa Bazoum “yana cike da karsashi” ko da yake har yanzu babu wutar lantarki a gidan da ake tsare da shi.
Kazalika tawagar, wadda ta je Nijar a karo na biyu domin yunkurin sulhu, ta gana da shugaban sojojin da suka yi juyin mulki Janar Abdourahamane Tchiani.
Wani dan jarida da ke aiki da kamfanin dillancin labarai na Nijar a fadar shugaban kasa ya tabbatar da ganawar.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM
They are not serious