JAMB Ta Tona Asirin Ɗalibar Da Aka Ba kyautar N3m Don Ta Ci 362

Hukumar shirya jarrabawar ta JAMB ta bayyana cewa, za ta dauki mataki kan wata dalibar da ta ce ta ci maki mai yawa.

Alfijir Labarai ta rawaito hukumar ta gano cewa, matashiyar ta samu maki 249 ne ba 362 da take yada ta samu ba, kamar yadda rahoto ya bayyana a baya, dalibar ta samu kyautar kudade daga wani kamfanin mota a Najeriya, lamarin da ya dauki hankali matuka.

JAMB ta ce za ta janye sakamakon jarrabawar da Ejikeme Joy Mmesoma ta yi na UTME.

Hukumar ta ce matashiyar ta samu maki 249 ne a jarabawar sabanin 362 da ta ke ta yadawa ta samu a baya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a Fabian Benjamin ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *