
Alfijr ta rawaito Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) za ta gudanar da nata zaben a mazabar Doguwa/Tudun Wada, a Kano.
Jami’in zaben mazabar tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai, ya sanar da hakan a ranar Laraba a hedkwatar hukumar da ke Kano yayin nazarin sakamakon zaben da aka gudanar a mazabar Doguwa/Tudun Wada na tarayya.

Idan zaku tuna INEC ba ta saka sunan Alhassan Ado Doguwa, dan takarar jam’iyyar APC a zaben wanda ya samu kuri’u mafi yawa ba, amma ta nuna cewa an bayyana sakamakon zaben ne ta hanyar tursasa Jami inta.
Yakasai ya ce hukumar ta sake duba sakamakon farko da ake zargin sa ya sanar bisa tirsasawa.
Ya ce INEC bisa tanade-tanaden dokar zabe ta sake duba sakamakon inda ya bayyana sakamakon da aka sake dubawa.
Farfesa Yakasai ya bayyana cewa sakamakon zaben da aka duba ya tsaya kamar haka, APC 39,732, NNPP 34, 798, PDP 7,091.

A cewarsa, an soke sakamakon zabe a rumfunan zabe 13.
Ya ce jimillar kuri’un da aka soke a rumfunan zabe da aka soke sun yi wa ‘yan takaran APC da NNPP rataya tazarar kuri’u.
Ya yi bayanin cewa adadin katin zabe da aka tattara a rumfunan zabe 13 da aka soke sun kai 6,917 sabanin kuri’u sama da 4,000 da ke tsakanin APC da NNPP.

Ya ce INEC za ta gudanar da karin zabuka a sassan da abin ya shafa domin tantance wanda ya lashe zaben mazabar tarayya na Doguwa/Tudun Wada da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
SOLACEBASE
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai