Inda Ba Kasa! Sakataren Hukumar Kimiyya Ta Kano Ya Karyata Ikirarin Badakalar Cefanar Da  kadarori 36.

FB IMG 1714148022250

Daga Aminu Bala Madobi

A kwanakin baya ne aka fara bincike kan babban sakataren hukumar kimiya da fasaha ta jihar Kano, Farfesa Dahiru Sale Muhammad, bisa zargin sayar da gidaje sama da 36 na hukumar ba tare da amincewar gwamnati ba.

Alfijir Labarai ta rawaito ana zargin Muhammad da bayar da sama da kadarorin gwamnati 36 da ke cikin garin Tiga da ke karamar hukumar Bebeji a jihar.

Sai dai kuma a wani martanin gaggawa da ya mayar kan zargin da akayi masa, Muhammad ya shaida wa manema labarai cewa duk zarge-zargen da ake yi masa ba shi da tushe balle makama, domin babu wani gida da ofishinsa ya sayar.

Ya ce: “Abin da ya faru dai shi ne, tsohon kwamishinan ilimi a gwamnatin Ganduje shi ne ya siyar da gidaje na hukumar kimiyya da fasaha, ba wannan gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba.

“Kamar yadda a lokacin da na kama aiki, babu wani abu kamar sayar da kowanne gidaje. Abin da na sani shi ne wasu ma’aikatan Kwalejin Technical Tiga sun kai karar shugaban makarantar a gaban kotu bisa zarginsa da sayar da gidaje, kuma kotu ta same shi da laifi, kuma an gurfanar da shi yadda ya kamata.”

Hakazalika, an tuhumi Sakataren zartarwa na hukumar da yin sauyi da tsige wasu shugabannin makaranta masu matakin aiki na 15 ba bisa ka’ida ba tare da zargin maye gurbinsu da abokai da ‘yan baranda wadanda ke kasa da matakin 12.

Da yake mayar da martani kan zargin, Muhammad ya bayyana cewa duk wadanda ya sauke daga mukamansu an same su da rashin cancantar shugabannin kwalejojin fasaha saboda ba su da kwarewa a fannin kimiyya da fasaha.

“Abin da muka yi shi ne sake tura wadannan rukunonin shugabanni wadanda ba su da cancantar da ake bukata da kuma nada kwararrun da ke da ilimin kimiyya da fasaha, kuma ko da hakan mun ba su abubuwan da muke son ganin sakamako. ”

Farfesa Dahiru Sale ya bayyana cewa yawancin kayan aikin darussan kimiyya da fasaha an ajiye su sama da shekaru 10 tun lokacin da gwamnatin Kwankwaso ta sayo su kuma ba a yi amfani da su ba.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *