Alfijr ta rawaito Tsohon Kwamishinan Addini na Jihar Kano, Dakta Muhammad Tahar Adam ya ce bisa radin kansa ya yi murabus daga mukaminsa, inda ya musanta rahoton cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ya sauke shi.
Idan za a iya tunawa kwamishinan yada labaran jihar Kano, Muhammad Garba ne ya fitar da sanarwa a ranar Asabar inda ya bayyana korar Dr Muhammad Tahar Adam wanda aka fi sani da “Baba Impossible” a matsayin kwamishinan harkokin addini.
A wata hira da ya yi da gidan rediyon Freedom “Baba Impossible” ya bayyana mamakinsa kan labarin korar sa inda ya bayyana cewa ya mika takardar murabus dinsa a ranar Juma’a, 30 ga watan Disamba, 2022 ga sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji.
Tsohon kwamishinan ya ce ya yi mamakin jin a kafafen yada labarai cewa ya maganar cire shi da ke yaɗawa karya ce karara.
Ya kara da cewa murabus din nasa ya dogara ne akan wasu dalilai na kashin kansa.
Baba Impossible ya ce, idan gwamnatin jihar ta ci gaba da yin karya game da shi, za a tilasta masa ya mayar da martani.
Sai dai a cikin sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai ya fitar, ”korar kwamishinan harkokin addini na nan take.”
Sanarwar ta kara da cewa, “Korar kwamishinan kuma dan majalisar zartarwar jihar ya biyo bayan, hali mara kyau a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati da ke rike da mukami mai ma’ana, da kuma kalamai marasa tsari.
Malam Garba ya yi nuni da cewa, an kuma same shi yana gudanar da al’amuran ofishinsa ne a matsayin sana’a, har ma yana rage ranakun aiki ga ma’aikatan ma’aikatar, inda ya kebe ranakun Laraba da Juma’a.
Kwamishinan ya kara da cewa baya ga gudanar da aiki ba tare da tuntubar juna ba, Baba Impossible baya biyayya ga gwamnati.
Ya bayyana cewa gwamnan ya aike da sunan Dr Nazifi Ishaq Bichi na Jami’ar Bayero Kano zuwa majalisar dokokin jihar domin maye gurbinsa.
Gwamnan ya yi wa kwamishinan da aka kora fatan alheri a ayyukan sa na gaba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇